Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wanda ya jagoranci sallar juma ya kara da cewa fitowar miliyoyin Al'umar a wannan rana ta juma'a ranar Qudus ta Duniya inda suke rera taken yin a…wadai ga Amurka a…wadai ga HKI na nuna cewa Al'ummar Iran ta tabatar da kawo goyon bayanta ga Al'ummar Palastinu.
Ayatul… Khatami yace zancen tattaunawa da azzalumar kasar Amurka keyi don kare manufofin HKI ne sannan wannan tattaunawa bata da wani shar'anci sannan ana yin hakan ne don tabbatar da HKI.
Dangana da makircin Amurka da HKI wajen sanya rarrabuwar kawunan Musulmi a Kasashen musulmi limamim ya bayyana cewa Amurka da HKI na amfani da makuddan kudade wajen amfani da wasu Mutane masu kafirta Al'ummar Musulmi inda suke kashe Musulmi a kasashen Iraki da Siriya don cumma manufarsu.
Dangane da rikicin siyasa a kasar Masar Limamin ya bayyana cewa ya kama Al'ummar Masar su zamanto masu basira ga makircin kasar Amurka da HKI sannan su bari juyin juya halin da su kayi ya zamanto kalkashin kasar Amurka.
Har ila yau limamin juma'a na birnin Tehran yayi a…wadai matakin da tarayyar Turai ta dauka na sanya kungiyar gogormawa ta Hizbil..labnan kan jerin kungiyoyin ta'addancin na Duniya kungiyar Hizbul…ta kare dukkanin kasar Labnan tare da Al'ummar kasar.
1266941