Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A nan kasar Iran an kammala shirye shirye na gudanar da zanga zangar a fiye da garuruwa da birane fiye da 700. Kuma miliyoyin Iraniyawa ne maza da mata zasu fito zanga zangar ta yau. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya ayyana ranar jumma’a ta karshe a cikin watan tamadan na ko wace shekara, a matsayin ranar Qudus ta duniya, ya kuma yi kira ga musulmi a ko ina suke duniya su nuna fushinsu ga mamayar kasar Palasdinu da kuma goyon bayansu ga Palasdinawa masu gwagwarmaya da HKI.
Ranar Qudus ta duniya ta bana dai, ta zo ne a dai dai lokacin gwamnatin kasar Amurka ta ke jagorantar wani taron sulhuntawa tsakanin gwamnatin HKI da kuma shugaban Palasdinawa Mahmood Abbas a birnin Washington na kasar ta Amurka.
Mafi yawan al-ummar Palasdinu dai suna adawa da wannan tattaunawan, musamman a dai dai lokacinda gwamnatin HKI take ci gaba da fadada gine gine a yankunan palasdinawan da take mammaye da su.
A nasa bangaren Zababben shugaban kasar Iran mai jiran gado Sheikh Hasan Ruhani ya bayyana mamayar Palasdinu a matsayin wani dadadden gyambo da ke jikin duniyar musulmi.
A furucinsa a yayin gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a jiya Juma'a; zababben shugaban kasar Iran mai jiran gado Sheikh Hasan Ruhani ya bayyana cewar ranar Qudus ta duniya, rana ce da take hada kan kasashen musulmi wajen fuskantar zalunci da babakere, kuma rana ce da take fayyace cewar al'ummar musulmin duniya ba zasu taba mance hakkinsu mai tsawon tarihi ba.
Sheikh Hasan Ruhani ya kara da cewar a daidai lokacin da duniyar musulmi ke fuskantar wasu 'yan matsaloli, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana kokarin yin amfani da wannan damar wajen gabatar da kanta a matsayin mai son zaman lafiya domin ta samu sukunin ci gaba da shimfida ayyukanta na zalunci da babakere.
Har ila yau Sheikh Ruhani ya fayyace cewar halartar zanga-zangar ranar Qudus ta duniya yana matsayin jaddada gagarumin goyon baya ne ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta.
1266881