Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni daga kasar Masar na nuni da cewa Majalisar gudanarwar kasar za ta yi wani zama, yayin da rikici tsakanin dakarun gwamnati da magoya bayan hambararren shugaba Morsi ke kara ta'azzara.
Fira Ministan rikon kwarya, Hazem el-Bablawi na tunanin rushe kungiyar ta 'Yan uwa Musulmi, wacce Mr Morsi memba ne a ciki. Mr Beblawi ya ce babu wani zancen sasantawa da mutanen da ke da hannu wajen zub da jini. A jiya Asabar ne jami'an tsaro suka fatattaki mutanen da ke cikin masallacin Al-Fateh a birnin Alkahira, inda magoya bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi suka kafa shingaye.
Jami'an tsaron na cewa sun cafke mutane da dama, ciki har da 'yan kasashen waje. Kana ana bincikar kimanin 250 daga cikinsu da ake zargi da aikata laifukan kisan kai da ta'addanci.
Jami'an tsaron Masar suna tsare da magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi musamman 'yan kungiyar Ihwanul-Muslimin da yawansu ya kai 250 kan zargin ayyukan ta'addanci.
A bayanin da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta fitar a jiya Asabar yana dauke da cewa: Rundunar 'yan sandan Masar tana tsare da 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Ihwanun-Muslimin fiye da 1,000 da ta kame bayan rikicin da ya kai ga hasarar rayukan mutane fiye da 100 a ranar Juma'ar da ta gabata.
A rahoton da kafar watsa labaran gwamnatin Masar MENA ya watsa a yammacin jiya Asabar ya bayyana cewar daga cikin magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi musamman 'yan kungiyar Ihwanun-Muslimin da jami'an tsaron Masar suka kame bayan rikicin ranar Juma'a, mutane kimanin 250 daga cikinsu ana zarginsu ne da hannu a aiwatar da kisan kai, kokarin aiwatar da kisa da kuma gudanar da ayyukan ta'addanci a kasa.
1274077