IQNA

An Bukaci Gurfanar Da Wadanda Suka Kashe ‘Yan Shi’a A Kotu A Masar

23:24 - November 24, 2014
Lambar Labari: 2611421
Bangaren kasa da kasa, mai kare mabiya mazhabar iylan gidan manzo a kasar Masar ya bukaci da a gurfanar da wadanda suke da hannu wajen yin kisan gilla a kan sheikh Hassan Shahata fiye da shekara guda da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun cewa lauya mai kare mabiya mazhabar iylan gidan manzo a kasar Masar ya gabatar da kukansa, tare da yin kira  da a gurfanar da wadanda suke da hannu wajen yin kisan gilla a kan sheikh Hassan Shahata fiye da shekara guda da ta gabata a lokacin da suke tarukansu na addini, inda ya ce yanzu duk wadanda suke da hannu wajen aikata wannan ta’addanci suna nan suna harkokinsu hankali kwance.

A nasa bangaren shugaban cibiyar addini  ta kasar Masar ya bayyana cewar babu wani dalili ko hujjar kafirta 'yan shi'a a cikin alkur'ani da hadisi ko kuma ingantattun littattafan Musulunci, kuma sabanin da ke tsakanin 'yan sunna da 'yan shi'a bai kai ga matakin kafirta juna ba, don  haka ya jaddada wajabcin samun hadin kai tsakanin dukkanin mazhabobin  Musulunci tare da nisantar duk wani abin da zai kai ga haifar da rikici a tsakaninsu.

Har ila yau shehin malamain ya jaddada cewar makiya Musulunci suna ci gaba da kulla makircin ganin sun haifar da rikici a tsakanin al'ummar musulmi, don haka dole ne a kan dukkanin musulmi su yi taka-tsantsan domin ganin ba su afka cikin tarkon makiya ba.

Tun bayan da 'yan salafiyya da wasu daga cikin 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood masu tsaurin ra'ayin addinin Islama suka dare kan karagar mulki a Masar suka fara ruruta rikicin mazhaba a kasar, kuma a 'yan kwanakin baya-bayan nan suka aiwatar da kisan gilla kan daya daga cikin shahararrun malaman shi'a a Masar Sheikh Hasan Shehata da almajiransa guda hudu a lardin Giza kusa da birnin Alkahira.

2610973

Abubuwan Da Ya Shafa: shahata
captcha