IQNA

Masu Da'awar Jihadi Na Daesh Suna Ci gaba Da Rusa Wurare Ibada Na 'Yan Sunnah Da Shi'a A Iraki

23:08 - November 27, 2014
Lambar Labari: 2612428
Bangaren kasa da kasa, 'yan ta'addan daesh da aka fi sani da ISIS suna ci gaba da rusa wurare na ibadar musuli da suka hada da sunnah da shi'a a kasar Iraki musamman wurare da suka kwace iko da su.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, ISIS suna ci gaba da rusa wurare na ibadar musuli da suka hada da sunnah da shi'a a kasar Iraki musamman wurare da suka kwace iko da su a arewacin kasar.
 
Rahotanni daga kasar Iraki na cewa 'yan ta'addan ISIS da ke da'awar jihadin kafa daular musulunci suna ci gaba da yanka 'yan sunna da suka ki ba hadin kai wajen gudanar da ayyukansu na ta'addanci a yankunan da suka kwace iko da su a rewacin kasar.  
Tashar talabijin ta kasar Iraki ta bayar da rahoton cewa, daga ranar Laraba da ta gabata zuwa jiya Lahadi, 'yan ta'addan na ISIS sun kashe mutane 322 dukkaninsu 'yan kabilar Bunamir a yankin Huwaijah, wadanda kuma dukkaninsu 'yan sunna ne, bisa hujjar cewa ba su ba su hadin kai, daga cikin wadanda ISIS ta kashe kuwa hard a mata da kananan yara, kungiyar kare hakkin bil adama ta tabbatar da wannan rahoto, tare da yin tir da Allawadai da wannan aikin dabbanci da 'yan ta'addan na ISIS suke aikatawa.
Har yanzu dai babu ko daya daga cikin kasashen larabawa da ta ce uffan kan kisan 'yan sunna da 'yan ta'addan na ISIS suke yi a halin yanzu a Iraki, duk kuwa da irin goyon bayan da suka rika baiwa kungiyar ido rufe a lokacin da ta fara kaddamar da hare-hare a da Iraki Iraki, bisa hujjoji na bangarancin mazhaba.

2612015

Abubuwan Da Ya Shafa: Irak
captcha