
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, a lokacin da yake kammala ziyarar da ya kai zuwa kasar Tukiya Paparoma Francis ya bayyana littafin kur'ani mai tsarki da cewa littafi ne na sulhu da ke yin kira zuwa ga zaman lafiya a tsakanin al'ummu, kuma addinin musulunci addini ne na kaunar juna da fahimta tsakaninsa da sauran addinai na duniya baki daya.
A lokacin da yake kammala ziyarar tasa jagoran na mabiya addinin kirista ya bayyana cewa, amsu fakewa da sunan addinin muslunci suna aikata ta'addaci bas u wakiltar musulmi, kuma dole ne kowa ya sanya, domin kuwa danganta abin da 'yan ta'adda suke da addinin muslunci cin fuska ne da cin zarafin wannan addini mai girma.
A lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin manyan malaman addinin musulunci an kasar Turkiya kuwa, jagoran na mabiya akiristanci ya ce yana da kyakyawar fahimta da irin abin da suke ji na daga bakin ciki da hankoron bata sunan addinin muslunci da 'yan ta'adda suke yi da sunanaddinin muslunci, ya ce kowane bangare a al'ummomin duniya na jin jina wa musulmi yadda suka zama masu hakuri da kuma kauda kai kana bin da ake yi musu sakamakon abin yan ta'adda suke, kuma yanzu duniya ta fara ganewa kuma kowa yana allawadai da 'yan ta'adda ne.
Paparoma Francis na daya dais hi ne jagoran kirista day a mayar da hankali wajen ganin ansamu hadin kai da fahmtar juna tsakanin kiristanco da addinin muslunci, tare da zaman lafiya tsakanin mabiya addininan biyu.