IQNA

Za A Gurfanar Da Wadanda Suka Kashe Sheikh Hassan Shahata Jagoran ‘yan Shia A Masar

23:51 - December 06, 2014
Lambar Labari: 2615763
Bangaren kasa da kasa, alkalin Aiman Abbas ya bayyana cewa za a gurfanar da mutanen da suke da hannu a kisan da ak yi wa sheikh Hassan Shuhat jagoran mabiya mazhabar shia a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-sharq cewa, Aiman Abbas alkalin kotun Masar ya bayyana cewa za a gurfanar da mutanen da suke da hannu a kisan da ak yi wa sheikh Hassan Shuhat jagoran mabiya mazhabar shia a Masar a shekara ta 2013 su 31 za su fuskanci hukunci a ranar 21 ga watan Disamba 2014.
Bayanin ya ci gaba da cewa wadannan mutane sun aikata abin da ya cancanci hukunci mai tsauri a kansa, domin kuwa sun kai hari kan fararen hula da suke gudanar da tarukan addini ba tare da yin barazana ga wani ba balantana zaman lafiyar kasa, amma a haka a ka yi musu kisan gilla a bainar jama’a har ma da jami’an tsaro suna kallo ba tare da sun tseratar da su ba, lamarin da ya saka alamar tamabaya kan wadanda suke mulki a lokacin karkashin inuwar kungiyar yan uwa musulmi.
Wannan mataki dai ya zo sakamakon nuna rashin amincewa da wasu manyan lauyyoyi na kasar Masar suka yi ne, bayan da mahukuntan kasar suka yi gum da bakunansu kan wannan lamari mai matukar hadari, dukkanin mutanen daioi an sansu, kamar yadda suka bayyana  acikin kamarori da suka dauki wannan aikin ta’addanci, kuma dukkansu za su gurfana  agaban kuliya.
2615177

Abubuwan Da Ya Shafa: shahata
captcha