IQNA

Jagororin Musulmin Australia Sun Yi Allawadai Da Garkuwa Da Mutane A Sydney

22:31 - December 15, 2014
Lambar Labari: 2618811
Bangaren kasa da kasa, jagororin mabiya addinin muslunci a kasar Australia sun yi Allawadai da kakakusar murya dangane da yin garkuwa da wasu mutane da wani mutum musulmi ya yi a birnin Sydney fadar mulkin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AAP cewa, a yau Ibrahim Muhammad jagoran mabiya addinin muslunci mazauna kasar Australia ya fitar da wani bayani da ke yi Allawadai da kakakusar murya dangane da yin garkuwa da wasu mutane da wani mutum musulmi ya yi a yau, tare da bayyana hakan a matsayin wani abu na bata sunan muslunci.

Yanzu haka dai ana ci gaba da zaman dar-dar a birnin Sydney na kasar Ausrtalia da wani mutum mai dauke da makamai ya yi garkuwa da mutane a cikin wani shago. Rahotannin da su ke fitowa daga kasar Austira sun ambato majiyar tsaron kasar na cewa; Wani mutum guda mai dauke da bakar tutar  kungiyar ‘yan ta’adda ta Isil, ya yi garkuwa da mutane da dama a cikin wani shagon shan Qahwa da ke birnin Sydney da safiyar yau litinin.

Bugu da kari, majiyar ‘yan sandan birnin na Sydney ta ce; “An rufe mashahurin dakin taron nan na Opraha da ke kusa da shagon da ake garkuwa da mutanen bisa dalilai na tsaro.” Tuni dai jami’an tsaro su ka killace hanyoyin da su ke isa shagon, abinda ya haddasa cunkoson ababen hawa a yankin.

Yin garkuwa da mutanen dai ya biyo bayan wani kankanen lokaci ne da ‘yan sandan birnin na Sydney su ka sanar da kame wani dan ta’adda guda da ya ke da niyyar kai hari a cikin kasar. Tuni dai pira minstan kasar ta Australia Tony Abbott ya kira yi taron gaggawa na majalisar tsaron kasar, domin tattaunawa abinda ya ke faruwa.

2618655

Abubuwan Da Ya Shafa: sydney
captcha