IQNA

Musulmin KenyaNa Ganin Cewa An Dokokin Yaki Da Ta’addancin Ne Domin Cin Zarafinsu

16:54 - December 27, 2014
Lambar Labari: 2636268
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Kenya na ganin cewa dokar yaki da ta’addancin da aka kafa akasar bayan kai harin yan ta’addan na Alshab na Somalia a cikin kasar an yi su ne kawai domin cin zarafinsu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, wasu daga cikin musulmin kasar Kenya na ganin cewa dokar yaki da ta’addancin da aka kafa akasar bayan kai harin yan ta’addan na Alshab na Somalia a cikin kasar an yi su ne domin tozartasu a kasar.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sanya hannu kan wata doka da ‘yan majalisar kasar suka kafa da nufin fada da ayyukan ta’addanci da addabi kasar duk kuwa da ci gaba sukan da ake yi wa dokar da ake ganin akwai yiyuwar ta share fagen take hakkokin bil’adama a kasar.  

A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin din kasar jim kadan bayan sanya hannu kan dokar, shugaba Kenyatta ya ce yana da tabbacin cewa dokar ba ta yi hannun riga da sauran dokoki wajen kare hakkokin bil’adama, yana mai cewa manufar dokar ita ce kare lafiya da dukiyar al’umma kasar Kenya. 
A shekaran jiya Alhamis ne dai ‘yan majalisar dokokin kasar Kenyan suka amince da dokar bayan muhawara mai zafin gaske da aka yi a majalisar lamarin da ya kai ‘yan adawa sun yi ature da kakakin majalisar da mataimakinsa.
Shugaba Kenyattan dai yana fuskantar matsin lamba ainun daga bangarori daban-daban na kasar kan ya yi wani abu don kawo karshen hare-haren ta’addancin da kasar take fuskanta mafi yawa daga wajen ‘yan kungiyar nan ta Al-Shabab ta kasar Somaliyan.
‘Yan adawan kasar dai sun ce za su daukaka kara a kotu kan wannan doka wacce suke ganin za ta share fagen take hakkokin al’ummar kasar musamman bangarenta da ya ba da umurnin hukunta kafafen watsa labaran da suke buga duk wani labarin da zai sanya mutanen kasar cikin tsoro da fargaba.
2636011

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha