IQNA

Wakilin Larabawa A Majalisar Isra’ila Ya Daga Tutar Palastinu A Masalalcin Quds

17:00 - January 06, 2015
Lambar Labari: 2678835
Bangaren kasa da kasa, wanda ke wakiltar larabawan palastinu a majalisar dokokin palastinu ya daga tutar ta palastinu a wurin taron maulidin manzon Allah a cikin masallacin Qods mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto  daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa Ahmad Tayyibi wanda ke wakiltar larabawan palastinu a majalisar dokokin palastinu ya daga tutar ta palastinu a wurin taron maulidin manzon Allah a cikin masallacin Qods domin nuna goyon bayansa ga palastinawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa wanann mataki na dan majalisar ya bakanta wa mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila matuka, an daya bangaren kuma tashar talabijin ta almanar ta bayar da rahoton cewa  jam’iyyar tauhid ta kasar ta yi kakakusar suka da yin Allawadai dangane da rufe masallacin Quds da yahudawan sahyuniya suka yi a cikin wannan mako domin hana musulmi gudanar da salla a cikinsa.
Rahotanni sun ce an sake bude masallacin bayan rufe shi da ‘yan sahayoniya su ka yi a jiya alhamis. Sanarwar rufe masalacin na kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a jiya alhamis ya fusata mazauna birnin na Qudus,kamar kuma yadda gwamnatin  Palastinawa ta bayyana shi a matsayin shelanta yaqi akan al’ummar Palastinu da kuma musulmin duniya.
Wannan kamfanin dillancin Labarun ya nakalto cewa; An sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Qudus bayan da a wunin jiya aka yi batakashi tsakanin matasa da jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila. Sai dai duk da bude masallacin kudus, yan sahayoniya sun gindaya sharadin cewa wadanda shekarunsu ba su kai 50 ba ba za su shiga masallacin ba domin yin sallar juma.
Irn wannan aiki na keta hurumin masalalicn Kudus dai ya zama wani abu da yahudawa ‘yan share wuri zauna su ke yi a kowace rana ta Allah ta hanyar kutsawa cikinsa. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rufe masallacin na Kudus, tun wanda ya faru a shekarar dubu da dari tara da sabain da shida kamar dai yadda rahoton ya tabbatar.
2676589

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha