
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Sheikh Na’in Qhasem mataimkain jagoran kungiyar Hizbullah ya bayyana a taron hadin kan musulmi cewa hankoron saka lamurra da batutuwa da suka danganci banbancin mazhaba a cikin lamurran na siyasa na daga cikin abubuwan da ya kamata a mayar da hankali kansu a wannan lokaci domin kuwa suna wargaza hadin kan al’ummar musulmi.
Malamai, masana da jami’an kasashen musulmi daban-daban sun kirayi al’ummar musulmi da su hada kansu waje guda don fuskantar makirce-makircen da makiyansu suke kulla musu.
Masanan sun yi wadannan kiraye-kirayen ne a lokacin da suke gabatar da jawabansu a wajen taron kasa da kasa kan hadin kan al’ummar musulmi da ake ci gaba da gudanar da shi a nan birnin Tehran.
A nasa bangaren shugaban majalisar amintattu na malaman musulmin kasar labn ya kirayi al’ummar musulmi da su yi taka tsantsan da akidar kafirta musulmi da aka shigo da shi cikinsu da nufin haifar da fitina a tsakanin musulmin, yana mai cewa irin wannan taron na hadin kai da ake gudanarwa wani mayar da martani ne ga masu yada wannan akidar ta kafirta musulmi.
Shi ma a nasa bangaren babban muftin kasar sham ya kirayi al’ummar musulmi da su yi koyi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran wacce ta sami damar karya katangar rarrabuwan kai tsakanin al’ummar musulmi yana mai jaddada matsayar gwamnatin Siriya na ci gaba da fada da ‘yan ta’addan da aka turo su kasar da nufin rarraba kan al’umma da kuma zubar da jininsu.
Shi kuwa shugaban majalisar siyasa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ja kunnen al’ummar musulmi ne da su yi taka tsantsan da sabon makircin da makiyansu suka kulla musu na rarraba kansu da hada su fada da junansu yana mai cewa shiga kasar Siriya da kungiyar Hizbullah ta yi wani shiri ne na fada da wannan makirci na rarraba kan al’ummar musulmin.
2683038