IQNA

Firayi Ministan Birtaniya Ya Halasta Cin Zarafin Addinai Da Yi Musu Izgili

16:55 - January 19, 2015
Lambar Labari: 2729266
Bangaren kasa da kasa, Firayi Ministan Birtaniya David Cameron ya ce al'ummomi masu 'yanci suna da hakkin su yi izgili da addini, a karkashin dokar 'yancin bayyana ra'ayi da fadar albarkacin baki.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, David Cameron firayi ministan Birtaniya ya ce al'ummomi masu 'yanci suna da hakkin su yi izgili da addini, a karkashin dokar 'yancin bayyana ra'ayi da fadar albarkacin baki a kasashen turai.
Keta alfarmar musulmi ya karu matuka a cikin kasashen turai a kasar Birtaniya ya karu da kasha goma cikin dari a cikin shekarun baya-bayan nan kamar dai yadda bayanin ya nuna.
A cikin wani bayanin na daban kuma wata babbar cibiyar musulmi ta dauki nauyin shirya wannan jin ra’ayin jama’a da kuma fitar da wannan sakamako da ke cewa cewa adadin mutanen adasuke karbar addinin muslunci a kasar Birtaniya a cikin shekaru goma da suka gabata ya nunka har sau biyu, wanda wata kila wannan ya harzuka masu kiyayya da musulmi.
Wasu da dama daga cikin fiye da kashi sittin wadannan mutane ne dai sun nuna cewa sun karbi muslunci ne sakamakon binciken da suke gudanarwa wanda haka ne yaba su damar daukar kudirin karbaer musulunci, sakamakon abin da suka gano a cikinsa na koyarwa ta hakika wadda mutum dan addam ke samun kamala da ita a cikin rayuwarsa ta duniya.
Babu shakka ana kokarin bata sunan sunan muslunci a turai da duniya ku wannan ya zo ne duk kuwa da cewa ana ta maganar ayyukan ta’addanci da ke bata sunan mus;nci sakamakon abin da ak shirya na bata sunan addinin ta hanyar yin amfani da wasu gurbatattun musulmin kuma bata gari, amma bayan bincike sun gane cewa addinin musulunci na zaman lafiya ne.
2726973

Abubuwan Da Ya Shafa: Cameron
captcha