IQNA

Dole Ne Musulmi Su Yi Amfani Da Hankali Wajen Fuskantar Cin Zarafin Manzo (SAW)

17:00 - January 27, 2015
Lambar Labari: 2770307
Bangaren kasa da kasa, babban malami mai bayar da fatawa a kasar Masar Shauki Allam ya bayyana cewa dole ne musulmi su yi amfani da hankali matuka wajen fuskatar cin zarafi da tozarcin da ake yi wa manzon Allah (SAW) a wannan lokaci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa, Shauki Allam babban malami mai bayar da fatawa a kasar Masar ya bayyana cewa dole ne musulmi su yi amfani da hankali matuka wajen fuskatar cin zarafi da ake yi wa manzon Allah a kasashen turai, ta yadda ba za a bayar da kafar wani cin mutuncin ba.
Wannan bayani na shehin malamin ya zo ne sakamakon matakin da wasu suka dauka na kaddamar da hare-hare kan ofishin jaridar da take cin zarafin amnzo, wanda hakan ya jawo wasu fitintunun na daban, a kan haka y ace ya kamata daukar duk wani mataki ya zama mai muhimamnci tare da yin amfani da hankali.
Kasashen turai dai sun yi amfani da wannan damar wajen nuna cikakken goyon bayansu ga wannan jaridar, inda suka taru suka goyi bayanta kana bin da take yin a cin zarafin manzo, wanda kuma abin bakin ciki shi ne yadda ya zama har da wasu daga cikin shugabannin kasashen musulmi.
Yanzu haka dai musulmia  koina cikin duniya suna ci gaba da nuna bacin ransu kan hakan tare da gudanar da jerin gwano, domin nuna takaicinsu kana bin da yake faruwa, musamman na cin zarafi.
2768905

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha