IQNA

An Kame Wasu Kokarin Sace Wani Kwafin Kur’ani Mai Tsarki A Alkahira

17:01 - February 01, 2015
Lambar Labari: 2794020
Bangaren kasa da kasa, an kame wasu mutane a lokacin da suke kokarin sace wani kwafin kur’ani mai tsarki na tarihi a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Alkahira akasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Radio Aljazairiyun cewa, a a yau ne aka kame wasu mutane a lokacin da suke kokarin sace wani kwafin kur’ani mai tsarki na tarihi a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Alkahira zuwa kasashen turai.
Ahmad Abulfadl shi ne shugaban bangaren bincike na shige da ficen kayayyaki a filin safka da tashin jiragen sama  akasar Masar musamman a birnin Alkahira, ya tabbatar da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike dangane da wannan lamari kamar dai yadda ya kamata.
Bayanin ya ci gaba da cewa an kame mutanen ne a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Alkahira a Masar, a lokacin da suke kokarin ficewa da dadden kwafin kur'ani na tarihi, da aka rubuta shi fiye da shekaru dubu da suka gabata a kasar ta Masar, a wato a hijira ta 391 Kamariyyah.
An bayyana kwafin kur’anin da cewa yana da tsawon 18.5cm da kuma fadinsa da ya kai 14cm, sai kuma gwabi shi ma 5cm kamar dai yadda mahukunta a bangare adana kayan tarihi na kasar suka tabbatar, wanda kuma tarihinsa ke komawa ga sheka ta 391 kamariyya wato bayan hijirar manzo.
2793745

Abubuwan Da Ya Shafa: Kuran
captcha