IQNA

Jerin Gwanon Kare Mabiya Addinin Musulunci A Yankin Wales

16:57 - February 02, 2015
Lambar Labari: 2798516
Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutane sun gudanar da jerin gwano a yankin Wales domin nuna goyon bayansu ga musulmi da kuma kin amincewa da gabar da ake nuna wa musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na South Wales Argus cewa, a jiya lahadi cincirindon mutane sun gudanar da jerin gwano a yankin Wales domin nuna goyon bayansu ga musulmi da kuma kin amincewa da gabar da ake nuna wa musulmi da ke zaune a yankin.
Aftab Shah daya ne daga cikin mabiya addinin muslunci a yankin, wanda ya nuna gamsuwarsu da jin dadinsu da irin wannan mataki da al’ummar yankin na Wales suka dauka na nuna rashin amincewarsu da abin da ake yi kan mabiya addinin muslunci.
Tun bayan abubuwan da suka faru na kai hari kan jaridar nan ta kasar faransa a cikin makonnin da suka gabata inda aka kashe babban iditan jaridar da kuma masu zanen batunci ga manzo a cikinta, wasu suka dauki karan tsana suka dora a kan musulmi.
Kasashen turai da dama an samu kungiyoyi da jam’iyuu masu adawa da musulunci da suka fito suna nuna adawarsu da addinin mulunci da kuma musulmi, amma kuma daga bisani an samu bullar wasu wadanda suka nuna rashin goyon bayansu ga haka, da hakan ya hada da har da a kasashen Jamus da sauaransu.
2797166

Abubuwan Da Ya Shafa: Wales
captcha