Kmafanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wefaq cewa, a jiya mutanen Bahrain sun gudanar da gangami a koina cikin kasar domin tunawa da ranar 14 ga Fabrairu 2011 da suka fara motsin neman sauyi daga salon mulkin zalunci da danniya irin na masaurautar Al-khalifah da ke mulkin kasar, duk kuwa da matakan danniya da nuna karfi a kansu.
Kwararru kan harkokin shari’a da kare hakkokin bil adama a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna damuwa matuka dangane da irin matakan da masarautar kasar Bahrain take dauka wajen murkushe ‘yan adawar siyasa a kasar, musamman ma tun bayan kame madugun adawa a kasar kuma babban sakaraen jam’iyyar adawar siyasa mafi girma a kasar Sheikh Ali Salman.
Mahukuntan na Bahrain dai sun kame Sheikh Ali Salman tun ranar ashirin da takwas ga watan disamban shekara da ta gabata, bisa hujjar cewa za su gudanar da bincike ne a kansa, amma tun daga lokacin suka saka a gidan kaso suna masu tuhumarsa da cewa yana kokarin kifar da masarautar kasar.
A cikin wani bayani da kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan wannan lamari a jiya, sun bayyana cewa dukkanin abin da masarutar Bahrain ke tuhumar Sheikh Ali Salman da shi kage ne na siyasa, kuma haka baya rasa nasaba da yunkurin da gidan sarautar kasar ke yi na murkushe mabiya mazhabar shi’a wadanda su ne kashi 86% na al’ummar kasar Bahrain, tare da nisantar da su daga duk wani sha’ani na siyasa ko tafiyar da mulki a kasar.
Tun a cikin Fabrairun shekara ta 2011 ne al’ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da gangami da jerin gwano domin neman a gudanar gyaran fuska dangane da yadda ake tafiyar da sha’anin mulki a kasar, inda suka bukaci sarki ya ci gaba da zama kan kujerarsa, amma a baiwa jama’a damar su zabi ‘yan majlaisar dokoki, ta yadda majalisar za ta zabi Firayi minista da kanta wanda zai kafa majalisar ministoci, kuma baiwa majalisar dama kafa kwamitin tsara kundin tsarin mulkin kasa wanda zai yi la’akari da hakkokin kowane bangare a kasar, maimakon yadda tsarin kasar yake na mulukiyyah, inda sarki shi ne wuka shi ne nama a komai, shi ne ke zabar Firayi minista da ministoci da ‘yan majalisa daidai da ra’ayinsa, ta yadda al’umma ba su da hakki a cikin hakan, bugu da kari kuma dukkanin mukamai a kasar mutane masu alaka da gidan sarautar ne ke rike da su, sauran jama’ar kasar kuma sun zama ‘yan kallo.
Bugu da kari kan hakan kuma al’ummar kasar Bahrain sun bukaci da a rika raba arzikin kasar bisa adalci, maimakon yadda lamarin yake a halin yanzu, baya ga dabaibaye sha’anin mulki da siyasa, hatta ma arzikin kasar na sarki da ‘yayan sarauta da masu alaka da su ne kawai.
Maimakon yin nazari dangane da wannan kira na al’umma, masarautar Bahrain ta gayyaci dubban sojoji daga Saudiyya da Jordan da kuma Hadaddiyar daular larabawa domin murkushe masu yin wannan kira, kuma tun daga lokacin da aka fara boren shekaru 4 da suka gabata ya zuwa yanzu, masarautar Bahrain tare da taimakon wadannan kasashe, sun kashe tare da jikkata dubban fararen hula da suka hada da maza da mata da kananan yara, tare da cin zarafin jama’a da rushe wuraren ibada da cibiyoyin ilimi.
Babban abin tambaya nan shi ne, mene dalilin da ya sanya kasashen yammacin turai yin gum da bakinsu kana bin da yake faruwa a Bahrain? A daidai lokacin da suke daukar nauyin kungiyoyin ‘yan ta’adda tare da abokansu daga cikin larabawa domin kifar da wasu gwamnatocin da ba su dasawa da su, kamar abin da ya faru a liya da kuma wanda ke faruwa a halin yanzu a kasar siriya a maimakon hakan ma wadannan kasashe su ne kan gaba wajen taimakon masaraurar Bahrain da muggan makamai domin murkushe mutane da suke neman gyara ta hanyar lumana da ba su taba daukar makami a kan gwamnati ba.
Babbar amsa dai ita ce kasashen yammacin turai ba al’ummomi ko maslahar al’ummomi ta dame su ba, abin da ke gabansu shi ne maslaharsu kawai, kuma za su bi dukkanin hanyoyin cimma wannan maslaha ko da kuwa zai kai ga kashe rayukan jama’a, kamar yadda suka yi a wasu kasashen a kuma suke yi a halin yanzu a wasu kasashen yankin, inda suke taimakon yan ta’adda a kan gwamnati, a Bahrain kuma suke taimakon gwamnati domin murkushe talakawa da ba su da kowa sai Allah.