IQNA

Manufar Kai Hari Kan Kibdawa Ita Ce Haifar Da Rikici Tsakanin Musulmi Da kirista

21:03 - February 18, 2015
Lambar Labari: 2868437
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Abdullatif Daryan babban malami mai bayar da fatawa a kasar Lebanon ya bayyana cewa manufar kai hari kan Kibdawa na da nasaba da yunkurin haifar da rikicin addinin musulmi da kuma kiristoci a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Al-nashrah ya habarta cewa, babban malamin kasar Lebanon nay an sunna ya bayyana cewa manufar kai hari kan Kibdawa na da nasaba da yunkurin haifar da rikicin addinin musulmi da kuma kiristoci a yankin gabas ta tsakiya.

Sakamakon wannan kisan da aka yi wa mutanen jiragen kasar Masar sun kaddamar da hare-hare da jijjifin safiyar yau a kan sansanonin mayakan kungiyar 'yan ta'adda na ISIS a cikin kasar Libya, bayan da kungiyar da cewa ta kashe wasu Kibdawan Masar 21 a kasar ta Libya.

Rundunar sojin kasar Masar ce ta sanar da hakana  cikin wani bayani da ta fitar a safiyar yau Litinin, inda ta ce harin ya nufi sansanonin 'yan ta'addan ISIS da kuma wasu runbun ada suke ajiye makamai, kuma a cewar bayanin dukkanin hare-haren an kaddamar da su a cikin nasara.

A jiya ne kungiyar ta ISIS da ke da'awar jihadi ta fitar da wani faifan bidiyo, wanda a cikinsa ta nuna yadda 'ya'yan kungiyar suka yi wa kibdawan Masar 21 yankan rago, lamarin da ke ci gaba da fuskantar kakkausar suka da Allah-wadai daga kasashen duniya.

2860809

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha