
Kamfanin dillancin labaran Iqn ay habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CNN Arabic cewa shugaban na kasar Amurka ya bayyana haka ne a yayin da ya ke gabatar da jawabi a gaban wakilan kasashe satin da su ke halartar taron ‘yaki da ta’addanci, da aka bude a fadar mulkin kasar.
Bugu da kari, shugaban na kasar Amurka ya ce; Dukkanin wadanda su ke yaki a karkashin kungiyar Isil, ‘yan ta’adda ne kuma wajibi ne duniya ta yi fada da tushen abinda ya ke maida mutane zama masu wuce gona da iri. Har ila yau shugaban na Amurka ya bayyana cewa; Yarda da cewa alka’ida da Isil ko Da’ish, suna da alaka da addinin Musulunci, tamakar amincewa ne da parpagandar da su ke yi. Wannan ba shi ne karon farko ba da shugaban na Amurka ya ke yin maganganun da su ke nuni da mika hannun kawance ga addinin Musulunci.
A shekarar dubu biyu da tara a birnin alkahira, shugaba Barrack Obama ya yi magana kwatankwacin wannan, haka nan kuma a yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na bayan nan. Sai dai a kasa, siyasar gwamnatin Amurka ba ta tafiya kafada da kafada da abinda shugaban kasar wanda mahaifinsa musulmi ne ya ke fada. Matsalar Amurka da al’ummar musulmi, ta rigayi zaman Barrack Obama shugaban kasa.
Daga lokacin da tarayyar Soviet ta rushe a gomiya ta casein na karnin da ya gabata, siyasar Amurka ta ginu ne akan maida addinin Musulunci ya zama wanda zai maye gurbin akidar kwaminisanci ta fuskar adadawa da shi.
A wancan tsakanin ne kuwa Amurkan ta fara share fagen wannan siyasar ta hanyar kulla kawance da alaka da kungiyoyi irin su alka’ida da kuma Taliban ta Afghanistan. A bisa abinda aka tsara shi ne cewa wadannan kungiyoyin za su zama masu yi wa manufofin Amurka aiki, sai dai daga lokacin da za su fita daga karkashin ikonsu, sai su ka maida hankali wajen bakanta sunan addinin Musulunci a idon duniya.
A cikin shekaru ashirin na bayan nan, yaduwar ayyukan ta’addanci da masu shi, ke fakew ada sunan Musulunci, sannan kuma a lokaci daya da abinda kasashen turai su key i na fada da addyukan ta’addancin, sun jefa kasashen musulmi cikin matsananciyar wahala, hrin sha daya ga satumba ya zama wani abu da Amurkan ta fake da shi domin watsa kin jinin Musulunci da musulmi a duniya.
Kuma a halin da ake ciki a yanzu sun bude filin dagar yakin da aka fi zubar da jini a tsakanin yake-yake na zamani, ba domin komai ba sai kokarin kifar da gwamnatin Basshar Assad na Syria. Suna kuma amfani ne da kungiyar “Dai’sh’ wacce ba wani aiki da ta ke yi da ya wuce bata sunan Musulunci.
Amurkan da kuma shugabannin nahiyar turai suna yin magana mai dadi a baki na cewa; ba su fada da addinin muslunci, sai dai a aikace siyasar kasashensu ta ginu akan adawa da addinin Musulunci.
Saboda haka magana ta fatar baki irin wannan ta Obama ba ita ce za ta sauya siyasar turai akan addinin Musulunci ba.