IQNA

Al'ummar Bahrain Na Gudanar Da Babban Jerin Gwano

22:35 - February 24, 2015
Lambar Labari: 2892667
Bangaren kasa da kasa, alummar kasar Bahrain suna gudanar da wani aggarumin jerin gwano domin nuna rashin amincewa da shari'ar zalunci a kan Sheikh Ali Salamn tare da neman a saki dukkanin fursunonin siyasa da ake tsare da su a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga tashar talabijin ta Alalam cewa, mutanen  Bahrain suna gudanar da wata gaggarumar zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da shari'ar zalunci a kan shugaban jam'iyyar adawa wifaq Sheikh Ali Salamn tare da neman a saki dukkanin fursunonin siyasa da ake tsare da su a kasar bisa zaluncin mahukunta.
Su dai mahukuntan na Bahrain dai sun kame Sheikh Ali Salman tun ranar ashirin da takwas ga watan disamban shekara da ta gabata, bisa hujjar cewa za su gudanar da bincike ne a kansa, amma tun daga lokacin suka saka a gidan kaso suna masu tuhumarsa da cewa yana kokarin kifar da masarautar kasar.
A cikin wani bayani da kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan wannan lamari a jiya, sun bayyana cewa dukkanin abin da masarutar Bahrain ke tuhumar Sheikh Ali Salman da shi kage ne na siyasa, kuma haka baya rasa nasaba da yunkurin da gidan sarautar kasar ke yi na murkushe mabiya mazhabar shi’a wadanda su ne kashi tamanin da shida na al’ummar kasar Bahrain, tare da nisantar da su daga duk wani sha’ani na siyasa ko tafiyar da mulki a kasar.
2889277

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha