IQNA

Malamin Ahlu Sunnah A Lebanon Ya Yi Suka Kan Yada Kiyayya Da Shi’a A Takanin Larabawa

23:50 - February 27, 2015
Lambar Labari: 2906473
Bangaren kasa da kasa, Malamin mabiya mazhabar Sunnah a Lebanon kuma babban sakataren cibiyar malaman gwagwarmaya Sheikh Mahir Hammud ya yi kakkausar suka da yin Allawadai dangane da yadda wasu suke ta kokarin yada kiyayya da mabiya mazhabar shi’a a cikin kasashen larabawa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa,a  wata zantawa da ya yi da tashar Almayadeen, Shekh Mahir Hammud ya yi kakkausar suka da yin Allawadai dangane da yadda wasu suke ta kokarin yada kiyayya da mabiya mazhabar shi’a a cikin kasashen larabawa a wannan lokaci, da nufin haifar da fitina da sunan banbancin mazhaba.
Malamin ya ci gaba da cewa duk inda aka samu wani mutum ko da yana kiran kansa malamai a cikin al’ummar musulmi kuma yana yada duk abin da zai haifar da fitina da rashin fahimtar juna tsakanin al’ummar musulmi, to tabbas wannan mutumin ko ya sani ko bai sani ba yana yi ma makiya musulunci aiki ne kai tsaye.
Ya kara da cewaa bin da yake faruwa  ahalin yanzu babban abin bakin ciki, yadda musulmi suka rafkana suka shiga dimuwa da fangima suka kasa gane ina suka dosa, ta yadda ya zama babbana bin da suke yia  halin yanzu shi ne fada da junasu da sunan banbancin mazhaba, kuma makiya bas u boye farincikinsu dangane da hakan.
A bangaren abin da ya shafi yan ta’adda kuwa,  malamin y ace bas u wakiltar al’ummar musulmi a abin da suke yi, ko da kuwa sun fake da wasu fatawoyi na wasu malamai da suke kafirta muuslmi bisa son ransu wadanda suka gabata, wannan shi ne musulunci ba, kuma basu wakiltar al’ummar musulmi balanta musulunci.
2904350

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha