IQNA

Fahimtar Juna Da Zaman Lafiya Shi Ne Babban sakon Addinin Muslunci

22:17 - March 03, 2015
Lambar Labari: 2921403
Bangaren kasa da kasa, tsohon babban mai bayar da fatawa a kasar Lebanon Sheikh Rashid Qabbani ya bayyana ayyuakn ta'addanci da cewa ba shi ne sakon muslunci na hakika ba.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nashrah cewa, tsohon babban mai bayar da fatawa a kasar Lebanon Sheikh Rashid Qabbani ya bayyana ayyuakn ta'addanci da ake aikatawa da sunan muslunci da cewa babban hadari ga shi kansa muslunci da kuma sauran mutanen duniya domin ba shi ne sakon muslunci na hakika ba.

Sheikh Rashid Qabbani ya ci gaba da cewa bayyana ayyukan ta'addanci a cikin wannan zamani yana da alaka da irin mummunar akidar da aka samar ne tun wasu karnoni da suka gabata, wadanda suke da alaka da fatawoyin kafirta musulmi tare da halastar da jininsu saboda banbancin fahimta a kan wasu mas’aloli.

Ya ci gaba da cewa nauyi da ya rataya kan malaman addinin muslunci da su mike wajen wayar da kan sauran mabiyansu da am al'umma baki daya, domin kwance kullin da aka kulla a cikin wanann mummuna akida ta kafirta musulmi, wadda kuma sakamakon abin da take dauke da shi ne ake ganin bayyana irin wadannan munan ayyka na ta'addanci da sunan musluncia.

A cikin yan lokutan nan dai yayan kungiyar suna ci gaba da kaddamar da hare-harensu na ta'addanci a cikin kasashen musulmi, inda suke kashe tare da yin yankan rago a kan fararen hula musulmi, da kuma kone su, duk da sunan jihadi a tafarkin ubangiji.
2918986

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha