Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Slabnews.com cewa, Sayyid Ali Fadhlollah a lokacin da yake gabatar da huduba a jiya, ya bayyana takaicinsa matuka dangane da matsyin wasu bangarori na malamai kana bin da yake faruwa akasar Iraki a cikin yan lokutan na yaki da ‘yan ta’adda.
Malamin ya ci gaba da cewa abin mamaki ne yadda wasu masu bayyana cewa suna goyon bayan hadin kan muslmi suke maganganu n araba kan musulmi dangane da sha’anin kasar Iraki, inda suke kokarin bayyana yakin da al’ummar kasar da dukkanin bangarointa ke yi da ‘yan ta’adda da cewa mabiya tafarkin iyalan gidan manzo suke yin hakan, kuma suna kashe ‘yan sunna yace, wannan abin takaici ne matuka.
Y ace da ya kamata a yi wa al’ummar Iraki adalci, domin kuwa masu yin wannan babban aiki suna yi ne domin Allah da kuma kubuytar da kasarsu daga halin da aka jefa ta, kuma dukkanin al’umma ce ta hadu a kan haka, kamar yadda ake gani a duk lokacin da suka samu nasara al’ummomin maza da mata da kanan yara suna yin farin ciki da yi musu addu’ar samun nasara.
Dangane da abin da yake faruwa a kasar Yeman kuwa, mamalin y ace tattaunawa da yin sulhu su kadai ne hanyar samun zaman lafiya da fahimtar juna a kasar, wanda kuma hakan na bukatar gudunmawar kowane bangare na kasar.
2979736