IQNA

Aana Jerin Gwanon Nuna Adawa Ga Masu Kyamar Musulunci A Faransa

23:16 - March 16, 2015
Lambar Labari: 2996920
Bangaren kasa da kasa, a cikin wannan mako an fara gudanar da gangami da jerin gwano a biranan kasar Faransa domin nuna adawa ga kungiyoyin da ke kyamar addinin muslunci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tsa_algerie cewa, wannan mako an fara gudanar da gangami da jerin gwano a biranan kasar Faransa domin nuna adawa ga kungiyoyin da ke kyamar addinin muslunci da suke gudanar da ayyukansu a cikin kasar.
A nasu bangaren mahukuntan kasar Faransa za su yi dubi dangane da wani korafi da mabiya addinin muslunci na kasar suka gabatar bisa la'akari da muhimmaiyar rawar da suke takawa wajen kawo zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al'ummomin kasar.

Ministan ya ce a cikin watan janairun da ya gabata an samu wasu masu tsattsauran ra'ayi a cikin kasar Faransa suna kai hari kan musulmin kasar, yayin da kuma acikin shekara ta dubu biyu da hudu an samu irin wannan yanayi marassa kyau, amma cewarsa suna daukar dukaknin matakan da suka dace domin kare rayukan musulmi da kuma dukiyoyinsu a kasar.

Ya ce mabiya addinin muslunci sun nuna dattijantaka matuka kana bin da ya faru, domin kuwa sun nuna rashin jin dadinsu dangane da hare-haren da aka kai a kasar, a kan babu dalilin da zai sanya su kuma a dauke su matsayin abokan gaba, musulmin faransa daidai suke da kowane dan kasa, suna da dukkanin hakkokinsu nay an kasa.

Dalil Bubakar limamin masalacin Paris ya ce suna bukatar a kare dukkanin hakokinsu ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu da sauran 'yan kasa ba.

2990501

Abubuwan Da Ya Shafa: musulmi
captcha