Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yanaklto daga shafin sadarwa na yanar gizo na (Aquila Style) cewa matar mai suna Vera mai shekaru 35 a duniya ta bayyana cewa ta hardace kur’ani mai tsarki ne a cikin wadannan shekaru duk kuwa da matsaloli da take fuskanta, kasantuwar kasar da take rayuwa, da kuma banbancin da ke akwai mai tazarra tsakanain harsunan larabci da kuma na kasarta.
Ta ce tana da fatan ganin ta samu damar koyar da sauran mutane da suka musulunta a kasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki, domin su ma su amfana daga irin falalolin da ke tattare da wannan littafi mai girma, da kuma kara fahimtar da su sahihiyar koyarwa ta addini.
Kimanin mutane 500000 ne daga cikin mabiya addinin muslunci suke rayuwa akasar ta Ukraine, kuma suna gudanar da harkokinsu na addini a dkkanin wuraren da suke.
3045217