IQNA

Harin Jiragen Saudiyya A kan Mashigar Ruwa Ta Babul Mandab

22:56 - April 03, 2015
Lambar Labari: 3081922
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin Saudiyya sun kaddamar da hari a kan mashigar nan ta babul Mandab a kasar Yemen hakan nan kuma sojojin kasar tare da taimakon sojin sa kai sun kwace iko da birnin Aden baki daya, kamar yadda aka halaka daya daga cikin sojojin Saudiyya masu gadin iyaka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aladdwaa.com cewa, a cikin hare-haren kwanaki 8 na Saudiyya a kasar Ymen fararen hula fiye da 100 sun rasa rayukansu da suka hada da 62 daga cikin kanan yara.
Rahotonni daga kasar ta Yemen suna bayyana cewa; Jiragen saman yakin gidan Sarautar Saudiyya da ke jagoranta rundunar hadin gwiwar wasu kasashen Larabawa da na ‘yan koransu suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankunan kasar Yemen musamman.

Hare-haren na yau suna zuwa ne kwana guda da jirgin saman yakin Saudiyya ya kai harin wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijiran Yemen a lardin Hujja da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fararen hula akalla 45 tare da jikkata wasu kimanin dari biyu da hamsin na daban.

Gidan talabijin din mayadin mai watsa shirye-shiryensa ta hanyar tauraron dan Adam ya bayyana cewa; Tun daga lokacin da gidan sarautar Saudiyya ya fara jagorantar kai hare-haren wuce gon da iri kan kasar Yemen yau cikon kwanaki na shida, an samu hasarar rayukan mutane fiye da dari daya tare da jikkatan wasu daruruwa na daban.

Sojojin Yemen da hadin gwiwar dakarun sa-kai musamman mayakan kungiyar Ansarullah ta mabiya Huthi sun samu nasarar tsarkake lardin Adan daga ‘yan ta’adda.

Rahotonni suna bayyana cewa: Sojojin Yemen da hadin gwiwar dakarun sa-kai musamman mayakan kungiyar Ansarullah ta mabiya Huthi sun samu nasarar tsarkake dukkanin lardin Adan daga ‘yan ta’addan kungiyar Al-Qa’ida da na ‘yan dabar tsohon shugaban kasar mai murabus.

Bayanai  sun tabbatar da cewa; Sojojin Yemen da na dakarun sa- kan duk da hare-haren wuce gona da iri da suke fuskanta daga jiragen saman yakin gidan sarautar Saudiyya sun samu nasarar kammala korar ‘yan ta’addan da na ‘yan dabar Mansur daga lardin Adan da yankunan lardunan Ma’arib da suke arewa maso gabashin kasar.

A halin yanzu haka dai hare-haren wuce gona da irin wasu kasashen Larabawa karkashin jagorancin gidan sarautar Saudiyya da taimakon Amurka kan kasar Yemen sun lashe rayukan mutane da yawansu ya doshi dari biyu tare da jikkata wasu daruruwa na daban.

3079848

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha