IQNA

Jami’ar Haward Ta Amurka Za Ta Shirya Wani Bayar Da horo Kan Ilmomin Muslunci

23:11 - April 03, 2015
Lambar Labari: 3082922
Bangaren kasa da kasa, jami’ard da ke kasar Amurka za ta shirya wani shiri na bayar da horo kan ilmomin addinin mulunci na gajeren zango.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Haward cewa, wanann jami’a za ta shirya wani shiri na bayar da horo kan ilmomin addinin mulunci na gajeren zango ga masu bukatar nean sanin wani danagne da mulsunci.

Wannan shiri y azo ne a daidai lokacin da ake kara samun mutane masu son sanin wani dangane da koyarwar addinin muslunci musamamn a bangaren falsafarsa da kuam kuma ilmin irfani a mahangarsa.

An samu dalibai da dama da suka yi rijistar sunayensu a wannan bangare da zai dauki nauyin shirya wanann bayar da horo, akasari wadanda suka yi rijistar mabiya addinin kirista ne, wadanda suke da matukar bukata dangane da sanin koyarwar wannan addini.

Kasar Amurka dai na daga cikin kasashen da jami’oinsu suke daukar nauyin shirya bayar da horo dangane da sanin mahangar addinai, duk kuwa da da cewa da dama cikin jami’oin kasar sukan ki shirya wani abu makamancin wanann wanda ya shafi addinin muslunci.

Ana kara samun masu fahimtar koyarwar muslunci a kasar, da suke gane cewa abin amahukunta ke sanar da su kan muslunci babu kamshin gaskiya a cikinsa, yayin da kuma wasu sanadiyyar hakan sukan muslunta.
3079847

Abubuwan Da Ya Shafa: Haward
captcha