IQNA

Mabiya Shi’a A Guinea Bissau Na Fuskantar Kora Daga Kasarsu

21:39 - April 11, 2015
Lambar Labari: 3124619
Bangaren kasa da kasa, masu tsatsauran ra’ayi da ke dauke da akidar wahabiyanci a kasar Guinea Bissau sun bayyna jiya Juma’a cewa ba su amince ‘yan shi’a si rayu a cikin kasarsu ba.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran Xin Huwa cewa, Karamba Bayu shugaban kungiyar matasan musulmi a kasar Guinea Bissau ya bayyana cewa ba za su rayu da mabiya mashabr shi’a ba tafarkin koyarwar addinin muslunci.
Shi ma a nasa bangaren Ibrima Sanha daya daga cikin mambobin majalisar shawara ta musulmin kasar ya bayyana wasu dalilai nasa na shirme da ke kokarin fitar da mabiya mazhabar iyalan gidan manzo daga addinin muslunci, ya kuma bkaci da a fitar da su daga kasar Guinea wadda ita ce kasarsu ta haihuwa.
Akasarin mabiya addinin muslunci a kasar Guinea dai yan sunna ne, amma kuma abin ban takaici shi ne yadda suka fada cikin tarkon wahabiyanci ta yadda suke kallon sauran musulmi a wajen addinin muslunci, wanmda hakan yake nuni da irin hadarin da mabiya mazhabar iyalan gidan manzo suke fuskanta a kasar.
Wahabiya suna cewa ba za su iya zama da yan shi’a ba wadanda suke tayar da hankula a kasashen Syria da Iraki, a kan haka sun bukaci da a kore su daga kasar baki daya, amma a nasu bangaren mabiya mahzbar iyalan gidan manzo sun kudiri aniyar shigar da kara kan wannan batu.
3121330

Abubuwan Da Ya Shafa: guinea
captcha