Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, wasu daga kafofin sadarwa na wabiyawa da ke karkashin gwamnatin Saudiyya sun shiga cikin shafin sadarwa na zumunta na tashar Alalam sun lalata wasu bangarorinsa.
Wadannan kafofin sadarwa sun dauki wannan mataki ne kan tashar ta Alalam sakamakon irin bayanan da take bayarwa kan kungiyar Ansarullah da kuma jagoran kungiyar Abdulmalik Alhuthi, wanda saudiyya ke bayar da bayanai na karya a kansa, da nufin kawo rudani a tsakanin mabiyansa.
Daga cikin fitattun tashoshin da suke yin wannan aiki na kokarin kara yada fitina tsakanin al’ummar musulmi na Yemen ta hanyar rahotanni na karya dangane da kungiyar har da talabijin ta Alarabiyya, mallamin gidan sarautar saudiyya.
Wannan ya sanya tashar ta Alalam daukar dukaknin matakai na ganin cewa ta fallasa duk wani labara na karya da tashihin wahabiya da nay an takfiriyya suke yadawa da nufin raunana gwiwar mutanen Yemen da suke fuskantar yaki daga gidan sarautar wahabiyan Saudiyya a cikin wannan lokaci.
Babbar manufar wahabiyawan dai ita ce kokarin saka shakku dangane da nasarar da suke samu, wanda kuma tun bayan fara kaddamar da hare-haren an wahabiyawa har bas u iya cimma ko daya daga cikin abubuwan da suka ambata ba, illa rusa gidajen jama’a da kashe kananan yara da mata.
Al’ummomin duniya dai na ci gaba da yin Allah wadai da wannan babban zalunci na gwamnatin wahabiya Saudiyya kan al’ummar Yemen marassa kariya, wadanda suke kokarin kare kansu da kuma sama kansu yanci daga danniyar azzaluman mahukunta.
3127804