Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kafar yada labaran Palastinawa, a jiya masu sanya ido kan hakkokin bil adama daga kasashen duniya daban-daban un bayyana haramtacciyar kasar Isra’ila a matsayin mai tauye hakkin kanann yara palastinawa.
Jami’an wannan cibiya mai sanya ido kan kare hakkin bil adama sun shiga cikin sansanonin palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jodan da kuma gabacin birnin qudus, domin gane ma idanunsu irin halin da palasrinawa suke ciki, inda suka ga cewa mutane suna cikin wahala, sakamamon danne hakkokinsu da yahudawa suka yi.
Daga nan kuma masu fafutukar sun isa wasu daga cikin matsigunnan yahudawa yan share wuri zauna, inda kuma a nan suka ga yadda yahudawa suke rayuwa a cikin walwala, yayin da suke bautar da palastinawa musamamn kanan yara daga cikin wajen yi musu ayyuka na wahala.
Bayanin kungiyar y ace da dama daga cikin palastinawan da suke aikia cikin matsugunna yaudawa kananan yara ne da suka kasa zuwa makaranta saboda rashin abin hannu, da kuma talauci ta yadda iyayensu ba su iya daukar nauyinsu balantan su yi karatu.
Kungiayr ta ce dole ne kasashe duniya su dauki matakin ladabtar da Isra’ila kan wannan lamari, ta hanyoyin takura tattalin arzikinta, da kaurace ma kayayyakin da take samarwa.
3140584