Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a jiya al'ummar kasar Yemen suna gudanar da bukukuwan cika shekaru 1430 da shigar musulunci a ckin kasarsu a daidai lokacin da jiragen yakin Al Saud ke lugudan wuta a kansu babu kakkautawa.
A cikin shekara ta 7 bayan hijirar manzon Allah ne addinin muslunci ya isa kasar Yemen, inda Imam Ali (AS) ya jagoranci kai addinin muslunci a kasar, wanda kuma a kowace sheakara ake gudanar da bukukuwan tunawa da wannan rana mai matukar muhimmanci a wajen al'ummar kasar Yemen.
Wannan shekara ana gudanar da tarukan ne a lokacin da ake lugudan wuta da masarautar Saudiyya ke yi a kansu, da nufin tilasta su bin manufofinta a yankin, wanda kuma hakan ya kara nisanta su da ita, da kuma kara jawo gaba mai tsanin daga al'ummar kasa a kanta.
Al'ummar kasar Yemen dai sun shahara da jarunta da kuma jajircewa kana bin da suka yi imani da shi, kuma yin amfani da kari a kans kan kara sanya musu taurin kai da kin mika wuya ga abokan gaba.