IQNA

Za A Fara Shirin Karatun Kur’ani Nas Kasa Da Kasa A Garin Kuita Na Pakistan

19:54 - May 04, 2015
Lambar Labari: 3255034
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wani shiri na karatun kir’ani mai tsarki na matasa mai taken debe kewa da kur’ani a kasar Pakistan.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, wannan taro na karatunkur’ani mai tsarki a garin Kuita dake cikin gundumar Baluchestan za a gudanar da shi ne tare da hakartar makaranta daga kasar Masar.

Samad Madani ya bayyana cewa, shi wannan shiri bababr manufarsa ita ce karfafa gwiwar matasa na yankin Baluchestaga harkokin kur’ani mai tsarki, musamman ma karatunsa, wanda shi ne zai bayar da dama wajen neman sanin saran bangarorinsa.

Wannan shiri dai ba zai takata da wuri dayba, makaranta na kasar Masar za su halarci wurare daban-daban da suka hada da makarantu da kuma masallatai domin domin gudanar da shirin na karatun kur’ani mai tare da halartar jama’ar yankin.

Ana fatan kuma wannan ya zama shi ne digon dan ban a wannan shiri a shekaru masu zuwa, domin amfanin matasa na kasar.

3247284

Abubuwan Da Ya Shafa: pakistan
captcha