Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nashrah cewa, Sheikh Mahir Abdulrazaq ya bayyana cewa dole ne malaman kasar Lebanon su san da cewa yada fitinar mazhaba a tsakanin musulmi ba maslaha ce ga al’ummar kasar ba.
Ya ce yana kira ga mahukuntan kasar Lebanon da su samu kyakyawan hadin gwaiwa da rundunar sojin kasar Syria domin kare kasar Lebanon daga hadarin yan ta’adda, wadanda a halin yanzu suka mayar da kasar babbar manufarsu, da nufin rusa ta.
Dnagane da masu hankoron mayar da batun barazanar da kasar ke fuskanta daga ‘yan ta’adda a matsayin batun bangaranci, malamain y ace suna yin kure, domin kuwa sai al’umma ta hadu karkashin tuta guda ta kasa ce za su iya kare kansu daga yan ta’adda, idan kuma bah aka ba, to kwa kasar na cikin hadari
Y ace yana kira ga dukkanin bangarori da su hadu karlashin jagorancin runduanr sojin kasar domin bayar da kariya ga kasar da kuma al’ummarta baki daya.
3260615