IQNA

Jiragen Yakin Saudiyyah Sun kai Harin Masallacin Imam Hadi (AS) Da ke Sa’ada A Yemen

21:42 - May 09, 2015
Lambar Labari: 3277829
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin Saudiyya sun kaddamar da hari kan masallacin mai dadden tarihi na Imam hadi (AS) da birnin Sa;adah a arewacin kasar Yemen.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-mayadeen cewa, a yau asabar jiragen yakin masarautar Al saud sun kaddamar da hare-hare kan masallacin mai dadden tarihi na Imam hadi (AS) da birnin Sa’adah a arewacin kasar ta Yemen da nufin rusa yankin baki daya.

Wannan hari y azo a lokacin da jiragen yakin na masarautar Saudiyyah suka harba makamai masu inzami 160 a yau a kan yankin Baka da ke garin na Sa’ada, lamarin da ya yi sanadiyyar rushewar Karin wasu wuraren tarihi da ke yankin.

Haka nan kuma jiragen na wahabiyawan Saudiyya sun harba makamai masu linzami 16 duk a yau a cikin birnin na Sa’adah, yayin da wasu majiyoyi suka ce mayakan na  kasar Yemen sun bayyana cewar dakarun kungiyar sun sami nasarar harbo wani jirgin yakin kasar Saudiyya samfurin Apache a yau din nan Asabar a lokacin da yake kai hare-haren a kasar.

Kafafen watsa labaran kasar  Yemen din sun jiyo majiyoyin kungiyar suna cewa  dakarun kungiyar sun sami nasarar kakkabo jirgin yakin Saudiyyan a yankin Baqam da ke lardin Sa’ada da ke arewacin kasar ta Yemen a lokacin da yake kai hare-hare a wajen, inda wasu majiyoyin suka ce an ma sami nasarar kame matukan jirgin su biyu.



3276783

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha