IQNA

23:49 - May 19, 2015
Lambar Labari: 3305570
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Asir jagoran kungiyar yan ta’addan salafiyya a kasar Lebanon ya bayyana yan ta’addan daesh da aka kashe da cewa suna daidai da sahabban manzon Allah (SAW)

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alhadas News cewa, mutumin da ake kira Ahmad Asir jagoran kungiyar yan ta’addan salafiyya a kasar Lebanon ya bayyana yan ta’addan daesh da aka kashe da cewa suna daidai ta fuskar matsayi da sahabban manzon Allah (SAW) saboda imaninsu.

 

Mutmin wanda ya shahara matka ta fuskar ayyukan ta’addanci, wanda kuma yake samun goyon baya baya daga gwamnatocin kasashen da suke daukar nauyin yan ta’addan salafiyya a cikin kasashen duniya musamamn kasashen larabawa, ya bayyana wannan ne a lokacin da ake nemansa ruwa jallo domin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Tun kafin wannan lokacin Asir ya jagoranci ayyukan ta’addanci da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kasar Lebanon da suka hada da jami’an tsaro da kuma fararen hula, wanda hakan ya kara tabbatar da cewa babbar manufarsu dai ita ce aiwatar da shairin makiya na rusa kasashen musulmi da na larabawa.

 

Yanzu haka dai malamai na ci gaba da mayar da martini dangane da wannan furuci da ya fito daga bakin wannan bababn ta’adda, msamamn malaman sunna daga cikinsu, wadanda suka mara masa  abaya a lokutan baya, tare da bayyana shia  matsayin mai gwagwarmayar sunna, wadanda wasunsu yanzu suke sukarsa saboda wanann furuci.

3305504

Abubuwan Da Ya Shafa: Lebanon
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: