IQNA

Al’ummar Yemen Ba Za Su Mika Kai Ga Manufofin Gwamnatin Saudiyyah Ba

23:46 - May 22, 2015
Lambar Labari: 3306374
Bangaren kasa da kasa, Allamah Sheikh Sahal Ibrahim Bin Aqil babban mai bayar da fatawa na Ahlusunnah a kasar Yemen ya bayyana cewa al’ummar kasar ba za su taba mika kai ga bakaken manufofin gwamnatin Saudiyyah ba.


Kamfanin dilalnin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Almayadeen cewa, Sheikh Sahal Ibrahim Bin Aqil  a zantawarsa da wannan tasha ya bayyana cewa al’ummar kasar ba za su taba mika kai ga bakaken manufofin gwamnatin Saudiyyah ban a kokarin shimfida ikonta a kan kasar.

Malamin ya ce za su bayar da cikakken goyon baya ga dakaru kasar da kuma sauran dakarun sa kai, domin kubutar da kasar da hankoron mamaya na kasar saudiyyah, wanda ya bayayna daga irin hare-haren wuce gona da irin dsa take kaddamarwa kan kasar a cikin wadannan lokuta.

Shi ma a nasa bangaren Wanda ya jagoranci sallar juma’a a wannan mako a  babban birnin jamhuriyar muslunci ya yi Allah wadai da laifukan yakin da kasar Saudiyya ta tafka a kasar Yemen.

Ya ce bBala’in da ya ke faruwa a cikin kasar Yemen a halin yanzu,  wadanda su ka haddasa shi sune masu kiran kansu, masu yin hidima ga wuraren biyu masu alfarma.

Har ila yau, limamin ya yi suka da kakkausar  murya akan murka wacce ta ke bugun kirji da kare hakkin bil’adama, amma ta yi shiru akan abinda ya ke faruwa a Saudiyya din saboda taimakon da ta ke baiwa Saudiyyar a yakin.

Ya kuma kara da cewa Saudiyyar ta shiga tsaka mai wuya saboda yakar Yamen da ta yi, wanda kuma shi ne zai kai ga faduwarta. 

Babban malamin na kasar Yemen y ace ba za su taba bari yan kungiyar alkaida su kafa gwamnati a kasarsu ba, kuma za su dauki dukkanin matakai na ganin hakan ba ta faru ba.

3306266

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha