IQNA

Malaman Shi’a Da Sunna A Lebanon Sun Yi Allawadai Da Hari Kan Yan Shi’a A Saudiyya

23:22 - May 23, 2015
Lambar Labari: 3306866
Bangaren kasa da kasa, malaman shi’a da sunna a kasar Lebanon sun yi kakakusar suka da yin Allawadai da harin ta’addanci da aka kai kan mabiya tafarkin shi’a a masallacin Imam Ali (AS) da ke Qatif a gabacin kasar saudiyya.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lebanon File cewa, Sayyid Ali Fadlollah ya bayyana cewa dukkanin malaman shi’a kasar Lebanon sun fitar da bayanai da ke yin kakakusar suka da yin Allawadai da harin ta’addanci da aka kai kan masallacin Imam Ali (AS) da ke yankin Qatif mabiya tafarkin shi’a a gabacin kasar saudiyya  a jiya juma’a.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da su ma mabiya tafarkin sunna suke yin Allawadai da wannan mummunan aiki na ta’addanci kan musulmi, inda malamai da daman a mabiya sunna  akasar ta Lebanon suka yi kakakusar suka a cikin bayanai daban-daban da suka fitar kan wannan lamari.

Sheikh Abdullatif Daryan shi ne bababn malamin mabiya sunna  nakasar Lebanon, ya yi tofin Alla tsine kan wanann hari, inda y ace yan ta’adda bas u wakiltar addinin muslunci balanatan sunanr manzon Allah, akan ya ce doloe ne Saudiyya gwamnati da jama’a su fito su dauki matakin shiga kafar wando daya masu aikata irin wannan ta’addanci da sunan addini, su daina ba su kariya.

Shi ma a nasa bangaren Sheikh Husam Al-ilani daya daga cikin malaman sunna a kasar ta Lebanon ya bayyana cewa, abin da ya faru a na harin ta’addanci kan masallata a jiya, ya kara fito da fuskar yan ta’adda, tare da banbance su da sauran musulmi masu bin koyarwar addini, domin kuwa duk wanda ya kai hari a masallaci dam aba shi da alaka da masalalci balanata abin da ak eyia  cikinsa.

Daga karshe ya yi kira ga mahukunta a cikin kasashen musulmi da su dauki matakan shiga kafar wando daya da wannan mummuna salon a aikin ta’addanci, na kai hari kan masallatai tare da kashe bayin Allah sun bautar ubangiji.

3306577

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha