IQNA

Malaman Saudiyyah Sun Allawadai da Hare-Haren Da Aka Kai Masallatan Shi’a

17:52 - June 05, 2015
Lambar Labari: 3311027
Bangaren kasa da kasa, Malami 92 daga malaman kasar Saudiyya sun kakkausar suka da yin Allawadai dangane harin ta’addancin da aka kai masalatan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allaha gabacin kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, Malamai 92 daga cikin malaman kasar Saudiyya ne suka fitar da bayani da ke yin kakkausar suka da yin Allawadai dangane harin ta’addancin da aka kai masalatan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allaha  gabacin kasar a cikin makonni biyu da suka gabata.

Wadanda suka saka hannu kan wannan bayani sun jadda cewa kungiyar ta’addancin na da ke kiran kanta daular musulunci a Iraki da Sham da ta dauki nauyin kai wannan hari, ba ta wakiltar mabiya tafarkin Sunnah, domin kuwa ta’addancinta bai takaita kan mabiya mazhabar shi’a, sun kashe yan sunna da dama a wurare da yawa.

A cikin makonni biyu da suka gabata dai an kai hare-haren ta’addanci a wurare daban-daban a cikin yankunan gabacin kasar ta Saudiyya, kuma wannan kungiya ta fito ta sanar da cewa it ace ke da alhakin kai wadannan hare-hare na rashin Imani.

Fu’ad Ibrahim wani marubuci a kasar saudiyyah ya bayyana cewa, abin da ya faru kuma yake ci gaba da faruwa sakamako ne na matsayar da ita kanta gwamnatin Saudiyyah ta dauka dangane da wannan batu, ta hanayar bayar da dama da malaman kasar wajen yada kiyayya ta banbanbcin mazhaba.

Ya kara da cewa idan da mahukuntan Saudiyya za su ajiye tsananin kiyayayr da suke da ita kan mabiya mazhabar shi’a kuma su yi mu’amala da su a matsayin kasa kamar kowa tare da kare hakkokinsu, da kuma daina yada gaba a tsaklanin muslumi saboda banbancin fahimta, to hakan ya ragu matuka.

3310991

Abubuwan Da Ya Shafa: saudi
captcha