IQNA

An Gudanar Da Wani Biki Mai Taken Kur’ani Da Daliban Jami’a A Khartum Sudan

22:33 - June 08, 2015
Lambar Labari: 3312266
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro mai taken kur’ani mai tsarki da kuma daliban jami’a a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sudan Vision Daily cewa, asusun da ke kula da harkokin daliban jami’ar kasar Sudan ta hanyar ba su tallafi ya shirya wani taro na dalibai na jami’a dangane da kur’ani mai tsarki.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shiri ya mayar da hankali wajen shirya gasar karatun kur’ani mai tsarki tsakanin daliban, tare da sauraren karatun kur’ani daga makaranta daga cikinsu, inda aka bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo daga cikinsu.

Babbar manufar wanann shiri dai ita karfafa gwiwar daliban wajen mayar da hankali ga lamurra da suka shafi kur’ani mai tsarki musamamn a cikin wannan lokaci da ake karatar watan Ramadan mai alfarma, wanda a cikinsa ake mayar da hanakali ga kur’ani.

Kasar Sudan dai na daga cikin kasashen musulmi da suke mayar da hankali ga lamurrana ddini, kasar da ke da mabiya addinin muslunci kashi 97 cikin dari na mutanen kasar.

3311961

Abubuwan Da Ya Shafa: sudan
captcha