IQNA

Daesh Ta Kahe ‘yan Sunna Fiye Da Sauran Bangarorin Alumma

17:52 - June 15, 2015
Lambar Labari: 3314807
Bangaren kasa da kasa, Sheikh naim Kasim mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa yan sunna ne suk fi zama abin layya a hannun ‘yan Daesh.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Almanar cewa, Sheikh Naim Kasim ya bayyana a wuron Muhamamd Ahamd Harb da ya yi shahada a Husainiya Alhalusiyyah, cewa yan ta’addan Daesh ba su bar wani bangare ban a al’umma dangane da ta’addancinsu, bil hasali ma yan sunna ne suka fi yawa a cikin wadanda suke kashwa.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabia wani taron tunawa da wani daya daga cikin wadanda suka yi shahada domin yaki da yan ta’addan an daesh, inda y ace mun ga dukkanin irin ayyukansu an ta’addanci a kan kowa, da hakan ya hada da su aknsu mabiya tafarkin sunna, kamar yadada cikin kwanakin nan mun ga yadda suka yi wa Duruz kisan gilla.

Ya ci gaba da cewaa cikin kasar Syria kowa ya san irin tabargazar da suka tafkawa, wanda hakan ya shafi hatta mabiya addinin kirista na wanann kasa, wadanda suke da tsohn tarihi da babu wani mahaluki mai musun haka, amma yan ta’adda sun tarwatsa su sun kasha sun yanka su babu gaira babu sabar.

Ya kara da cewa anui ne da ya rataya kan dukaknin bangarorin musulmi su mike domin yaki da wannan balai daya addabi al’umma, matukar dai ana bukatar zaman lafiya a cikin kasashen msuulmi da na larbawa, tare da taka birki ga wadanda suke daukar nauyinsu.

3314795

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha