Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, mahardata 146 ne suka shiga bangare na karshe na gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da kuma tajwidinsa a birnin Ribat na Magrib.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ana gudanar da ita a duk lokacin azumin watan Ramadan mai alfarma, inda makaranta da mahardata daga sassa na kasar kan halarci wurin, domin nuna irin baiwar da Allah ya yi musu.
Muhammad Al-zayani shi ne babban mai kula da alkalnacin gasar tare da sauran masu taimaka masa, ya bayyana ccewa babbar manufar gasar dai ita ce kara ma matasa karfin gwiwa wajen mayar da hankali ga lamrra da suka shafi kur’ani mai tsarki.
Y ace akwai alkalan gasar da aka gayyata daga sassa na kasar, wadanda kwararru ne kan lamurra da suka shafi alkalan gasar kur’ani, ta fuskar sanin kaidojin karatu da kuma kiyaye su yadda ya kamata bisa ilmin tajwidin kur’ani mai tsarki.
A kan babu wata damuwa dangane da alkancin gasar, kuma wannan lamari ya tasiri matuka domin kuwa awannan shwkara an samu karuwar masu halartar gasar daga yankuna na kasar, kamar yadda aka samu hakan a shekarar da ta gabata, amma shekarar bana ta dara ta bara.
Dag akarshne gasar mutane 34 ne za su isa matakin kusa da na karshe, wadanda a cikinsu ne za a fitar da matakai na daya da na biyu har zuwa na biyar, kuma za a ba su kyutuka kamar yadda aka saba yi.
3322775