Habib Sadaqat wakilin Iran a gasar Kur’ai ta duniya a Turkiya a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bbana cewa,a wanann karo an fitar da sabbin kaidoji na gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Turkiya ta wannan shekara da hakan ya hada da cewa, mai karatu ba zai wuce mituna 10 ba baki daya dole ne ya tsaya, kuma ba dole ne mai karatu ya zama ya hardace dukkanin kur’ani ba.
Hakan an kuma wajen bayar da maki dole ne ayi la;akari da wasu lamurra, da suka hada kyawun karatu da kuma sauti, da yadda mai karatu yake kiyaye kaidojin karatun wato tajwidi da kuma fitar da haruffa yadda ya kamata, zai samu maki 60, hakan kuma bangaren kyawun sauti zai samu maki 40 daidai.
Ya ci gaba da cewa wannan karo ga dukkanin alamu za a samu babban ci gaba ta wannan fuska, domin kuwa dukkanin alkalan da suke jagorantar alkalancin gasar suna bin wannan kaida da kuma sharudda da aka gindaya a gasar karatun kur’ani ta bana.
Wakilin an Iran a wannan gasa ya ce babban abin da ke da muhimamnci shi ne kiyaye kaidji na karatu da fitar da sauti yadda ya kamata tare da kiyaye kaidojin karatun, idan mutum ya kiyaye hakan to sauran kaidojin ma zai kiyaye su kai tsaye domin tare suke tafiya.
Habib Sadaqat da kuma Aba Zar Karami su ne masu wakiltar kasar Iran a wannan gasa a wannanshekara.
3325877