Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lebanon Files cewa, Sheikh Abdul amir Qabalan mataimakin shugaban majalisar shi’a akasar Lebanon, a lokacin da yake ganawa da Khalid Shahab shugaban kungiyar injiniyoyin kasar Lebanon a jiya, ya cewa dole e zama cikin lura dangane da hadarin da ke tatatre da bazuwar ayyukan ta’addanci a cikin yankin baki daya.
Ya ci gaba da wannan hadari guda biyu ne da al’umma take fuskanta, wato hadarin yan ta’’ada da kuma masu ta’addanci da lasisi wato yahudawan sahyuniya na Isra’ila, wadanda suke a matsayin babbar barazana ga al’ummomin musulmi da na larabawa baki daya.
Malamin ya ci gaba da cewa jama’ar kasar suna da cikakkiyar masaniya dangane da irin barnar da yahudawan sahyuniya suka yi musu, wadanda kuma a halin yanzu suke kawance da yan ta’adda domin rusa kasar da ma sauran kasashe masu yancin siyasa a yankin.
A kan haka ya yi kira musamman gam asana da su zama suna da masaniya kana bin da yake faruwa na daga makircin da ake shirya ma al’ummar yankin baki daya, domin kauce ma fadawa cikin tarkon da ake dana msu, wanda kai iya kaiwa ga rushewar al’umma.
3332005