Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Irish Times cewa, wannan jerin gwano mai taken (ba da suna na ba) ya gudana ne a birnin Dublin fadar mulkin Ireland.
Bayanin ya ci gaba da cewa musulmin wadanda suka hada da kungiyoyinsu da kuma majalisar musulmin Najeriya mazauna yankin duk sun sanya hannu kan wata takarda, wadda take yin kira da a fahimci cewa addinin muslunci da musulmi ba su da wata alaka da kungiyar ‘yan ta’addan IS.
Takardar dai ta kunshi muhimman abubuwa da suka hada da bayyana hakikanin abin da ake kira da addinin muslunci ga wadabda bas u sani, shi addini ne zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai na duniya, ba tashin hankali kamar yadda wasu suke daukarsa ba.
Mabiya addinin muslunci na yankin sun sha alawashin ci gaba da wayar da kan al’umma a yankin, domin kada su fada cikin tarkon da aka dana na bata sunan addinin muslunci da da’addanci, ta hanya nuna ayyuakn yan ta’adda a matsayin su ne koyawar muslunci.
Musulmin Ireland suka ce ba za su bari a yi amfani da sunan addinin muslunci wajen bayyana ayyakan ta’addanci a matsayin koyarwarsa, za su ci gaba da gudanar da duk abin da ya sawaka na wayar da kai, da kuma kara nisanta muslunci daga duk mummunan aiki da ake danganta masa.
3334830