IQNA

Mai Bayar Da Fatawa A Masar Ya Yi Allawadai Da Kisan Jariri Da Sahyuniyawa Suka Yi

23:56 - August 02, 2015
Lambar Labari: 3338095
Bangaren kasa da kasa, Shauki Allam babban mai bayar da fatawa a kasar Masar baki daya ya yi kakkausar suka dangane da kone jaririn da yahudawan sahyuniya suka yi a palastine.


Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, Shauki Allam babban mai bayar da fatawa a kasar Masar ya yi kakkausar suka dangane da kone jaririn da yahudawan sahyuniya suka yi tare da bayyana hakan da cewa aiki na ta’addanci da dabbanci.

Ko shakka babu abin da ya faru manuniya ce kan irin mawuyacin halin da al’ummar palastinu suke rayuwa a cikinsa karkashin mamayar Isra’ila, domin kuwa wannan ba shi ne karo na farko da irin hakan take faruwa ba, lamurra da dama da suka fi haka muni sun faru a kan al’ummar palastinu ba tare da sun samu wani dauki ba, hatta daga ‘yan uwansu kasashen larabawa ba.

Kisan wannan jariri ya zaburar da lamirin al’ummomin duniya wajen nuna kiyayya kan zaluncin da al’ummar palastinu ke fuskanta, wanda hakan ya kara saka Haramtacciyar kasar Isra’ila cikin matsin lamba mai tsanani, wanda kuma zai kara barin mummunan tasiri a mahangar al’ummomin duniya dangane da siyasarta.

A ranar Juma’a da ta gabata ce dai yahudawan sahyuniya suka kashe wani karamin yaro dan watanni 18 tare da jikatta dan uwansa dan shekaru 4 da haihuwa, ta hanyar kona su da wuta.

3337687

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha