IQNA

Kiran Azhar Zuwa Ga Tattunawa Tsakan Sunnah Da Shi’a Domin Kashe Fitina

22:31 - August 03, 2015
Lambar Labari: 3338552
Bangaren kasa da kasa, Kamal Halbawi ya bayyana cewa kiran da cibiyar Azhar ta yi na gudanar da tattaunawa bayan yarjeeniyar Iran da 5+1 tsakanin Sunnah da shi’a domin kashe wutar fitina da sunan addini ne.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadaraw na yanar gioz na Alqabs cewa, Kamal Halbawi masani dan kasar Masar, kuma shugaban cibiyar hadin kan musulmi a Birtaniya ya yi ishara da cewa, wannan kiranm da cibiyar Azhar ta yi na gudanar da tattaunawa tsakanin Sunnah da shi’a yana da matukar muhimamnci.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu hada karfi da karfe tsakanin dukkanin bangarorin musulmi musamamn ma shi’a da Sunnah lamari ne mai kyau da ya kamata a kara bayar da himma  akansa domin ganin ya tabbata, domin hakan ne kawai zai bayar da dama domin kawo karshen ta’addanci da sunan addini.

Abdullah Al-sinawi dangane da muhimamncin da ke tattare da hakan ya ce akwai wasu daga cikin bangarorin musulmi da suke yin amfani da wannan dsama da suka samu ta barakar da ke tsakanin mabiya addinin musulunci wajen yada akidarsu ta kafirta musulmi.

A cikin wannan mako ne dai cibiyar Azhar ta fitar da bayani da ke yin kira da a gdanar da zaman a musamman tsakanin dukkanin bangarori na addini musamman ma tsakanin Sunnah da shi’a, domin samun bakin zaren warware matsaloli da dama da ke ci ma musulmi tuwo a kwarya a wannan zamani.

Hassan Nafi’a daya daga cikin malaman ilmimin kimiyyar siyasa a jami’ar Kahira ya bayyana cewa wannan kira yan ada matukar muhimmanci, kuma ya zama wajibi a mayar da hankali kan hakan, domin samun maslaha tsakanin al’ummar musulmi baki daya.

Ya ce tun a zamanin Sheikh Shaltut aka bijiro da wannan batu na samun zama da daidaito tsakanin bangarorin musulmi snna da shi’a, domin warware da dama daga cikin mas’alolin addinin muslunci.

3338338

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha