IQNA

Kin Amincewa Da Mayar Da Masallcin Shi’a Makabarta / Bayanin Malamai kan kame Sheikh Hassan Isa

21:52 - August 21, 2015
Lambar Labari: 3349569
Bangaren kasa da kasa, an gangamin nuna kin amincew da mayar da masallacin Sheikh Aziz makabarta tare da yin Allawadai da kame Sheikh Hassan Isa da yin kira da a gaggauta sakinsa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na 14f2011.com cewa dubban mutane sun gudanar da jerin a gwano a sassa daban-daban na kasar Bahrain, domin yin Allawadai da kakkausar murya dangane da hankoron mahukuntan kasar na rushe masallacin Shi’a  na sheikh Aziz zuwa makabarta.

Wadanda suka gdanar da jerin gwanon suna dauke da hotunan shehin malamin da kuma kyallaye da aka yi rubutu a kansu, da ke yin Allawadai da gidan sarautar kasar, da ke cin zarafin fararen hular kasar da ke neman a yi a dalci da gaskiya a cikin sha'anin mulki da siyasar kasar, maimakon mayar al'umma saniyar ware, ta yadda sarki da 'ya'yansa da mukarrabasa ne kawai suke da ikon mulki da kuma mallakar arzikin kasa.

Kin amincewar malaman Bahrain da cin zarafin Sheikh Hassan Isa

Malamai a kasar sun nuna rashin amincewa da cin zarafin daya daga cikin malamai kuma tsohon dan majalisa daga jam’iyyar Alwefaq, haka nan kuma masu jerin gwanon sun sha alwashin cewa ba za su taba amincewa da cin zarafin malamai da ke fada wa sarakuna da masu mulki gaskiya ba, haka nan kuma masu zanga-zangar sun kirayi masarautar kasar da ta gaggauta sakin shugaban jam'iyyar Hadaka ta alwifagh, wanda ake tsare da shi sakamakon gwagwarmayar nema wa talakawan kasar 'yancinsu, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa suna ci gaba da yin kiraye-kiraye ga masauar Bahrain da ta gaggauta sakin Sheikh Salman da ma sauran fursunonin siyasa da take tsare da su.

Masarautar kasar Bahrain ta sake kame sheikh Hassan Isa ne a ranar Asabar da ta gabata bayan da ya soki mahukuntan kasar dangane da yadda suke cin zarafin 'yan adam a gidajen kaso.



Kwamitin kare hakkin bil adama na Bahrain ya bukaci sako Sheikh Hassan Isa



Shafin sadarwa na Manama Post ya ce, masu kare hakkin bil adama sun ce babu dailin kame malamin domin kuwa abin da aka yin a siyasa ne saboda matsayarsa takin amincewa da zaluncin da masarautar kasar key i ne kan fararen hula.

Mahukuntan na Bahrain dai sun kame Sheikh Ali Salman tun disamban da ya gabata bisa hujjar cewa za su gudanar da bincike ne a kansa, amma tun daga lokacin suka saka a gidan kaso suna masu tuhumarsa da cewa yana kokarin kifar da masarautar kasar.

Kwararru kan harkokin shari’a da kare hakkokin bil adama a Majalisar Dinkin Duniya sun nuna damuwa matuka dangane da irin matakan da masarautar kasar Bahrain take dauka wajen murkushe ‘yan adawar siyasa a kasar, musamman ma tun bayan kame madugun adawa a kasar, kuma sun sha alwashin bin kadun lamarin sheikh Hassan Isa.



3349458

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha