IQNA

Musulmi Sun Kafa Cibiyar Samar Da Sulhu Tsakanin Al’ummar Kasar Kenya

23:47 - August 29, 2015
Lambar Labari: 3353837
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Kenya a Nairobi sun kafa wata cibiya wadda za ta rika gudanar da ayyuka na sasanta tsakanin mutane masu rashin jutuwa a kasar.


Kafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Standard Media cewa, Ibrahim Abdullahi shi ne shugaban wannan cibiya, wadda y ace muhimmin aikinta shi ne zagayawa domin daidaita tsakanin mutane masu rashin fahimta a sassa na kasar ta Kenya.

Ya ci gabada cewa mutane 47 ne cikin mabiya addinin muslunci a kasar suke cikin tawagar matafiya wadanda za su aikin cibiyar wadda za ta rika gudanar da ayyuka na sasanta tsakanin mutane masu rashin jutuwa a kasar a dukkanin garuruwa da kauyuka na kasar.

Babban burin dai shi ne isar da sakon zaman lafiya da sulhu irin na addinin muslunci, maimakon bayyana wannan adini a matsayin nay an tashin hankali da rashin son zaman lafiya kamar yadda wasu suka dauka bisa ga abin da ake gaya musu ko kuma suke jin ana fada.

Abdullahi ya ci gaba da cewa abin da yan ta’adda suke yi da sunan muslunci ko kadan bai dace ba da koyar addinin muslunci, wanda adini ne na zamn lafiya da sulhu da kuma fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai baki daya.

Dangane da abin wadanda mutane suke aikatawa da sunan muslunci yace, ya kamata duk wanda bai san addini bay a koma yay i karatun sa domin kada ya halaka.

3353553

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha