IQNA

23:37 - August 30, 2015
Lambar Labari: 3354281
Bangaren kasa da kasa, jaridar Disra ta kasar Italiya ta bayar da rahoton cewa Abu Nedal shugaban majalisar juyin ta Fata ya kashe Imam Musa Sadr da abikan tafiyarsa bisa umarnin Gaddafi.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya bhabarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-diyar cewa, jaridar Disra ta kasar Italiya ta buga wani sabon rahoto dangane da makomar Imam Musa Sadr a lokacin da ake gudanar da tarukan cika shekaru 37 da bacewarsa.

Jaridar Disra ta ce Abu Nedal wanda shi ne ya kashe dubban mutane da suka da sabani da Gaddafi shi ne wanda aka dira ma alhakin kashe Imam musa Sadr tare da abokan tafiyarsa.

Jaridar ta ce a wani zama da aka gudanar tsakanin Abu Nedal da wasu mutane biyar wadanda da shi kadai suke da alaka, a nan suka tattanawa yadda za su kashe Imam musa Sadr bisa umarnin da Gaddafi ya bayar kan hakan, bayan sun kammala ganawa da shi ba da jimawa ba, an tafi da Imam Musa Sadr zuwa wani mai tzarar kilo mita dari daga birnin Tripoli, inda  anan ake kashe wadanda suke adawa da Gaddafi a lokacin.

Bayan isarsu sun kwanton bauna kan tawagar da ke tare da shi, daga nan Abu Nedal da tawagarsa suka bde musu wuta suka kashe, kuma suka bizne sua  wurin, bayan kwanaki biyar Abu Nedal ya dawo birnin Tripoli ya sanar da Gaddafi cewa an aiwatar da aikin da ya sanya su.

Daga nan kuma sai hukumar liken asiri ta kasar Libya ta sanar da cewa Imam Musa sadr yta tafi Italiya, kuma bisa umarnin Barloskoni ya sanya hannu kan fasfo na Imam Musadr da abokan tafiyarsa kan cewa sun isa kasar Italiya domin  wawantar da hankulan al’ummomin duniya.

Jaridar ta ce Abu Nedal ya aiwatar da hakan ne bisa hadin baki tsakanin Gaddafi da wasu daga cikin manyan kasashen yankin, cewa a halaka Imam musa Sadr, kuma jaridar ta samu wannan bayanin ne daga tsohon shugaban hukumar liken asiri ta Libya bayan kame a kasar Mauriyania kafin a mika ga sabbin mahukuntan kasar.

3353919

Abubuwan Da Ya Shafa: Lebanon
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: