Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, alhazan yankin zirin Gaza guda 2450 ne za su bi ta wannan mashiga har tsawon kwanaki 3 a jere.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun bayan juyin mulkin da aka yi wa tsohon shugaban kasar Masar Muhammad Morsi 2013, mahukuntan kasar suka dauki kwararan matakai kan yankin Rafaha da kuma mashirsa domin yaki da ayyukan ta’addanci.
Bayanin ya ci gaba da cewa yana daya daga cikin irin abubuwan da suka yi ta faruwa na takura ma alummar Palastinu da suke a cikin kasar ta wannan mashiga da sunan ayyukan tsaro,.
Yanzu haka dai akwai alahazai na yankin da suka riga suka shiga cikin kasar ta masar daga can kuma zuwa kasa mai tsarki domin safke faralin bana, duk kuwa da ce3wa an kayyade lokacin da za su iya bi ta yankin.
Wannan mataki na mahukuntan Masar suna fiskantar kakausar suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasashen duniya daban-daban, tare da bayyana hakan amatsayin danne akkokin al’ummar yankin.
3360961