IQNA

21:56 - September 13, 2015
Lambar Labari: 3362168
Bangaren kasa da kasa, babban daraktan ISESCo Da kuma babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen msuulmi sun isar da sakon taya alhini ga iyalan wadanda ski rasa rayukansu a hadarin da ya faru a Makka.


Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC-OCI.org cewa kungiyar hadin kan akasashen musulmi ta nuna alhini da kuma isa da ta’ziya ga iyalan wadanda suka rasu 107 da kuma alhini ga fiye da 200 da suka samu raunuka a hadarin na harami.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban abin damuwa da ya kada zukatan dukkanin musulmi a koina tare da fatan Allah ya yi gafara ga wadanda suka rasu da kuma kawo sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka.

Kungiyar ISESCO ta isar da sakon taya alhini kana bin da ya faru a Makka

Rahotanni sun ce Abdulaziz Usman Al-tuijari babban sakaren ISESCO ya isa da ta’aziya kan wannan lamari, inda maniyyata dari da bakwai suka riga mu gidan gaskia, kana wasu da dama suka jikkata sanadin fadowar wani karfen injin lodin kayan gini a masalacin Ka’aba ko Harami a Makka. kawo yanzu babu cikaken bayani daga mahukuntan kassar.

3361831

Abubuwan Da Ya Shafa: Mekka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: